News
Wani Magajin Gari A Ƙasar Faransa Ya Kafa Dokar Hana Sauro Shawagi A Cikin Garin
Magajin garin Saint-Just-Saint-Rambert a yankin Loire na Faransa ya fitar da wata doka mai ban dariya, inda ya hana sauro masu ratsin baki da fari shawagi a cikin garin.
Magajin garin, Olivier Joly, ya ce ya dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe da dama daga mazauna yankin kan cizon sauro da matsalar da suke haddasawa.
Dokar ta bayyana cewa duk wani sauro mai ratsin baki da fari da aka samu yana shawagi a garin ya kamata ya dakatar da hakan, yayin da aka kuma ce masu karya dokar na iya fuskantar hukunci.
Sai dai matakin na magajin garin na dauke da barkwanci, domin manufarsa ita ce jawo hankalin jama’a kan bukatar daukar matakan dakile yawaitar sauro.
Joly ya ce wasu mazauna garin sun koka da cewa ba sa iya zama a waje cikin kwanciyar hankali saboda cizon sauro,
Rahotanni sun ce har yanzu babu wani sauro da aka kama ko aka ci tarar sa tun bayan kafa dokar.
-
News22 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
