Connect with us

News

CUTAR MASHAKO: Gwamnatin Filato Ta Umarci A Rufe Makarantu A Fadin jihar

Published

on

1788132611689

Gwamnatin Jihar Filato ta umarci rufe dukkan makarantun firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu, a faɗin jihar, domin dakile yaɗuwar cutar mashaƙo.

Umarnin zai fara aiki daga Litinin, 7 ga Satumba, 2026, kuma ya shafi makarantun da suka riga suka koma karatu.

Gobara Ta Lalata Gidaje Shida A Kasuwar Kofar Wambai Da Ke Kano

Kwamishiniyar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta ce an ɗauki matakin ne bayan samun rahotannin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a wasu sassan jihar.

Ta ce an samu rahotannin cutar musamman a ƙananan hukumomin Jos ta Arewa, Wase, Jos ta Kudu da Bassa.

Gwamnatin ta ce rufe makarantun na ɗan lokaci ne domin kare lafiyar ɗalibai, malamai da sauran ma’aikatan makarantu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin shawo kan cutar.

Advertisement

 

CHANNELSTV

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending