News
Gobara Ta Lalata Gidaje Shida A Kasuwar Kofar Wambai Da Ke Kano
Gobara ta lalata wasu shaguna da ɗakunan ajiya da ke cikin gine-gine shida a sashen ‘Yan Robobi na Kasuwar Kofar Wambai da ke Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:43 na daren Juma’a, inda gobarar ta tashi a bene na sama na wani gini da ake amfani da shi wajen sayar da robobi da kuma ajiyar kayayyaki.
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce shaguna huɗu, ɗakunan ajiya shida da rumfunan wucin gadi huɗu sun samu mummunar illa sakamakon gobarar.
Jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar dake Rijiyar Zaki, Sabon Gari, Government House da Bompai ne suka yi aikin kashe gobarar, inda suka yi nasarar hana ta bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar.
Hukumar ta ce binciken farko ya nuna cewa na’urar mai amfani da hasken rana ce ta haddasa gobarar.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
