News
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 36, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Da Dama
Dakarun Soji sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ’yan ta’adda da dama a sabbin hare-haren da suka gudanar a sassan ƙasar.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, inda ta ce ayyukan sojin sun gudana tsakanin 31 ga Agusta zuwa 3 ga Satumba, 2026.
Neman Kuɗin Aure Ne Yasa Na Shiga Harkar Garkuwa Da Mutane —Wanda Ake Zargi
Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro kan ayyukan soji da hulɗa da kafafen yaɗa labarai, Manjo-Janar Michael Onoja, ya ce dakarun sun kai samame kan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, masu safarar makamai da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a wurare daban-daban.
Ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci a jihohin Borno da Yobe, inda suka samu nasarar kashe wasu ’yan ta’adda tare da dakile hanyoyin safarar kayayyakin da suke amfani da su.
Onoja ya ce a ranar 1 ga Satumba, sojoji sun kashe wani ɗan ta’adda bayan sun tarwatsa wani bam da aka dasa a kan hanyar Miyanti-Banki Junction da ke Bama a Jihar Borno.
A yayin samamen, an kwato bindigogi da harsasai, in ji shi.
A Jihar Yobe kuwa, ya ce an kashe wani ɗan ta’adda yayin wani artabu a Lamusuri Crossing Point da ke Gujba, inda aka kwato bindiga da harsasai.
Kakakin ya ce a ranar 31 ga Agusta, dakarun sun kama wani ɗan ta’adda da ya tsere daga gidan yari a kusa da Sabsawa, Bama.
Ya kuma ce sojoji sun kama wani mutum da ake zargi da safarar kayan abinci a Konduga, inda ake zargin cewa kayan na zuwa wani yanki da ’yan ta’adda ke Bama.
A cewar Onoja, dakarun sun kuma kama wani mutum da ake zargi tsohon ɗan ta’adda ne, wanda daga baya ya zama mai ba da bayanai ga jami’an tsaro a Damasak, ƙaramar hukumar Mobbar ta Jihar Borno.
Ya ƙara da cewa wasu mayakan ’yan ta’adda da dama sun mika wuya tsakanin 1 zuwa 2 ga Satumba.
Haka kuma, an kama wasu da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki da kuma wasu da ake zargi da leƙen asiri.
Hedikwatar Tsaro ta ce dakarun na ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a sassan ƙasar.
-
News21 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
