News
Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Dubu 13 Da 500 – Badaru Abubakar
Ministan Tsaro na Tarayya, Mohammed Badaru Abubakar, ya ce dakarun Najeriya sun kashe fiye da ‘yan ta’adda 13,500 tun bayan hawar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake bayani kan nasarorin da gwamnatin ta samu a bangaren tsaro cikin shekara biyu da suka gabata.
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Kafafen Yaɗa Labarai Kan Tallata ’Yan Ta’adda
Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji matsanancin kalubale a fannin tsaro, amma yanzu abubuwa sun inganta sosai, musamman a yankin Arewa maso Gabas da wasu sassa na kasar.
A cewarsa, “A baya idan aka ce Gambaru ko Bama, mutane kan firgita saboda barazanar ‘yan ta’adda, amma yanzu komai ya canza. Haka nan hanyar Abuja zuwa Kaduna da ke fama da garkuwa da mutane yanzu ta dawo lafiya.”
Ministan ya ce tun daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda sama da 13,500, inda kuma suka hallaka sama da shugabannin Boko Haram 300 a fadin Najeriya.
Ya kara da cewa a yankin Kudu maso Gabas, jami’an tsaro sun kama wata mota dauke da katan 18,000 na harsasai da fakiti 250 na wasu makamai masu hadari.
A bangaren kama masu aikata laifi, Badaru ya ce an cafke ‘yan ta’adda 17,469, tare da ceto mutane 9,821 da suka fada hannun miyagu. Haka kuma an gano wani wuri da ake kera bindigogi a Jihar Filato, inda aka lalata makamai da dama.
Ministan ya ce ficewar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga ECOWAS ba ta shafi tsaron Najeriya ba, saboda matakan da gwamnati ta dauka na hadin gwiwa da jami’an tsaro a kan iyakokin kasar.
Ya ce gwamnati na kokarin dakile yaduwar matsalar tsaro zuwa Kudu maso Yamma, ta hanyar dakatar da motsin ‘yan ta’adda daga yanki zuwa yanki.
