Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Masallatai Ana Tsaka Da Yin Sallar Juma’a A Katsina 

Published

on

Yan ta’adda sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a Katsina

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wasu yan ta’adda da ake kyautata zatun  yan Bindiga ne  dauke da muggan makamai sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a garin Dan-Ali na karamar hukumar Dan musa dake jihar Katsina.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa maharan sun kai farmaki masallatai masu yawa lokacin da mutane suke tsaka da yin Sallar juma’a.

Advertisement

“Cire Harajin VAT Na Makamashi Yana Da Kyau -Yola

Haka zalika yan ta’addan sun mamaye masallata tare da bude wuta akan mutanen garin , hakan tasa dole masu yin Sallar jumma a gudun neman tsira da rayuwar su

Jaridar PUNCH  ta ruwaito cewa mazauna garin sun ji harbin bindiga lokacin da suke yin Sallar jumma a, inda kowa ya gudu Kuma ba’a kai ga kammala Sallar ba.

Advertisement

Kawo lokacin rubuta Wannan labari ba’a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina akan faruwar lamarin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending