News
Shugaba Tinubu ya bai wa Kakakin Majalisa Tajudeen lambar girma ta GCON
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sauya lambar girman da ya bai wa kakakin majalisar wakilan ƙasar zuwa GCON bayan ‘yan majalisar sun nuna rashin jin daɗinsu.
Yayin jawabinsa na Ranar ‘Yanci a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya sanar da karrama wasu manyan ƙasar ciki har da Kakakin Majalisa Tajedeen Abbas da lambar girma ta CFR, yayin da aka bai wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ta GCON.
Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Masallatai Ana Tsaka Da Yin Sallar Juma’a A Katsina
GCON ce lamba ta biyu mafi girma a Najeriya bayan GCFR.
Sai dai hakan ya jawo muhawara a majalisar wakilan a ranar Laraba, inda wakilan suka nemi shugaban ya sauya wa jagoran nasu da lamba mafi girma.
“A madadin haka, [shugaban] ya amine ya sauya wa kakakin lambar da GCON maimakon CFR kamar yadda aka saba,” a cewar wata sanarwa a yau Juma’a da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta ce ‘yanmajalisar sun jawo hankalin shugaban ƙasar kuma ya yanke shawarar gyara “kuskuren da aka yi na saɓa wa daɗaɗɗiyar al’ada”.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
