News
“Cire Harajin VAT Na Makamashi Yana Da Kyau -Yola
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Masana tattalin arziki irinsu Dakta Abdulnasir Turawa Yola na ganin cire harajin VAT akan Iskar Gas, Man Dizel da kuma na CNG abu ne me kyau, kuma hakan zai saukaka hauhawar farashi a Najeriya, idan har gwamnatin tayi abun da ya dace.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matakin cire harajin VAT zai saukaka lamura acikin Najeriya.
Sanatocin Arewacin Najeriya 12 Da Suka Gaza Gabatar Da Ƙudiri A Watanni 15 — Rahoto
Mista Wale Edun, wanda shi ne Ministan kudi, ya ce wannan sabbin matakai da suka dauka za su rage radadin tsadar rayuwa da al’ummar kasar ke fama da shi.
Edun ya kara da cewa, matakan za su taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki, sufuri da dai sauransu.
Sai dai ‘yan Najeriya dai na ganin daukar wannan matakai kadai ba za su kai su gacci ba.
Haka zalika a ɓangaren masana tattalin arziki irinsu Dakta Dakta Abdulnasir Turawa Yola na ganin cire harajin VAT da Gwamnati ta yi akan Man Dizel da Iskar Gas, abu ne me kyau, kuma hakan zai saukaka hauhawar farashi a kasar, idan har gwamnatin tayi abun da ya dace.
Wannan ci gaban dai ya zo ne a daidai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya ke korafin tsadar rayuwa a kasar, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 32.15 cikin 100 a watan Agustan 2024.Wannan ci gaban dai ya zo ne a daidai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya ke korafin tsadar rayuwa a kasar, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 32.15 cikin 100 a watan Agustan 2024.
