News
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Cire Harajin Gas Din Girki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta sanar da yin sassaucin haraji akan wasu abubuwan da suka shafi man Diesel da iskar Gas don samar da kyakyawan yanayin kasuwacin fannin.
Gwamnatin tace daga yanzu ta jingine batun karbar harajin siyan kayayyaki wanda aka fi sani da VAT akan Gas din girki da wanda ake yin amfani da shi a abubuwan hawa.
TA LEKO TA KOMA A KUMBOTSO: Jam’iyyar NNPP ta canja dan takarar shugaban karamar hukuma
Ministan kudi Wale Edun, ne ya fitar da sanarwar hakan a jiya laraba.
Ministan ya fitar da sanarwar ta hannun shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Muhammad Manga, inda yace hakan zai taimakawa Nigeria wajen cimma manufar habbaka samar da iskar Gas, da mamashi.
Wannan ci gaban dai ya zo ne a daidai lokacin da akasarin ‘yan Najeriya ke korafin tsadar rayuwa a kasar, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 32.15 cikin 100 a watan Agustan 2024.
