Connect with us

News

Kudin Kilon Gas Din Girki Ya Kai N1,200

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

’Yan Najeriya na kokawa kan tashin gwauron zabon gas din girki inda farashin kilo ke kaiwa N1,000 zuwa N1,200.

 

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa wasu cibiyoyin sayar da gas, yake N1,000, duk da cewa akwai masu sayarwa a kan 950, sai masu N880.

Tashin gwauron zabon gas din ya sa mutane kan yi tafiya mai nisa domin zuwa inda suke ganin za su samu da suke, ko da yake ba lallai hakarsu ta cimma ruwa ba.

Advertisement

 

Wata mata mai suna Suwaiba Ola da ta yi takanas daga Jihar Ogun zuwa Legas domin cika tukunyar gas dinta mai nauyin kilo 12.5 ta ce, “Tun daga Mowe na zo nan (Legas) na sayi kilo 12.5.

Advertisement

 

“N1,150 zuwa N1,200 ake sayar da duk kilo, saboda haka 12.5 zai iya haura N12,000, wanda ya yi tsada sosai, gaskiya da wuya idan zan iya ci gaba da kashe irin wadannan kudaden wajen sayen gas din girki.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending