News
Farashin Buhun Gawayi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Mazauna Birnin Kano sun koka kan yadda sukace farashin gawayi ya yi tashin gwauron zabo a wannan lokacin.
A halin yanzu farashin dauri daya na gawayi ya tashi zuwa N200, daga N100 da ake sayar da shi a makonnin baya.
Buhun gawayin kuma ya tashi daga N4500 ya koma Naira 6300 a sarin kowanne buhun guda saboda yawan amfani da shi
INDA RANKA ta ruwaito cewa an samu karuwar yadda mutane ke yin tururuwar amfani da gawayi a wurare daban-daban sakamakon tsadar farashin gas.
Wani mai sayar gawayi a unguwar Tudun Yola dake Kano, Malam Sani Umar ya ce daman in dai lokacin damuna ya zo ana samun tashin farashin gawayi.
Yace duk a irin wannan lokacin na ruwan sama ana samun karin farashi saboda Karancin shigo dashi daga cikin daji
Malam Umar Mai gawayi ya Kara alakanta tashin gawayin da zanga-zangar tsadar rayuwa da yan Najeriya suka gudanar inda aka samu kirin Naira 800 a duk buhu.
Haka zalika ya kara da cewa yanzu kasuwar tasu taja baya inda ya ce ada kusan kowanne gidan da suke siyan gawayi suna girki sau uku ko hudu a kowacce rana Amma yanzu baifi ayi sau Biyu ba
