News
Dan Mu Ba Tela Bane Hasali Ma Bai Taba Hawa Keken Dinki Ba —Iyalan Matashin Da DSS Ta Kama
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yan uwan Matashin Da Jami’an Tsaro suka kama Suke zarginsa da Dinka tutar Ƙasar Russia sun bayyana Cewa Matashin ba tela bane Kuma Bai taba yin dinki ba.
Yan uwan Matashin sun bayyana Damuwarsu akan Yadda Jami’an Tsaro suka kama Matashin Tare da Zargin Cewa Shine Yake Dinka tutar
Kotu Ta Tura Jagororin Zanga-Zanga Gidan Gyaran Hali A Katsina
Suna Mai Cewa Matashin Mai Suna Ahmad Yusuf Muhammad, Bai Shiga Zanga Zangar da akayi ba, Sakamakon Gargadi da Iyayensa Sukayi Masa
Amma acewar Yan uwan nasa Sunyi Mamakin Yadda Jami’an Tsaro suka Ce, wai Shine Yake Dinka tutar Ƙasar ta Russia
Ta Yaya Wanda Bai Taba dinki ba, Kuma Bashi da Keke Kuma ace an kama shi Amatsayin Wanda Yake Dinka tutar? acewar Yan uwan Matashin
Sun Bukaci Jami’an Tsaro Suka bincike akan Wadanda Ake Zargin Tare da Kira da Saki Dan uwan nasu, Tunda acewar su Bashi da alaka da Abinda ake Zargin sa Dashi.
Daily Trust ta rawaito abaya bayan nan ne Jami’an Tsaro suka Kama Mutane da yawa da Laifin Daga Tutar Ƙasar Russia, ciki harda Matashin da Yan uwansa Suka Ce, Bashi da Hannun
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
