Connect with us

News

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon 2023 

Published

on

Neco

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon 2023 na daliban da suka zana jarabawar tare da samun kashi 61.6 na wadanda suka samu Ingilishi da Lissafi.

Da yake fitar da sakamakon a ranar Talata, magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce jimillar dalibai 1,196,985 ne suka zauna zana jarabawar.

Advertisement

Auren Zawarawa: Ranar Juma’a Za A Dauran Auren Zawara A kano

Ya ce daga cikin jimillar dalibai da suka zauna jarabawar, 737,308 sun samu nasara da kiredit biyar zuwa sama da suka hada da harshen Ingilishi da lissafi, wanda ke wakiltar kashi 61.60 cikin 100 na dalibai 1,196,985 kuma sun cancanci shiga jami’a

A wani labarin kuma Auren Zawarawa: Ranar Juma’a Za A Dauran Auren Zawara A kano

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending