Connect with us

News

Ɗalibin Da Aka Kama Da Laifin Satar Amsa Za A Haramta Masa Shiga Kowace Jarabawa  Na Tsawon Shekaru Uku — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Satar amsa

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki sabon mataki na ladabtarwa da nufin dakile yawaitar satar amsa a jarrabawar ƙasa, inda ta sanar da cewa duk ɗalibin da aka kama da laifin satar amsa za a haramta masa shiga kowace jarraba ta ƙasa har na tsawon shekaru uku.

Ministan Ilimi na Ƙasa, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarni, wanda Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Advertisement

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kabo : Manuniya Kan Kyawun Alaka Tsakanin Shugaba Tinubu Da Sanata Barau

A cewar mai magana da yawun JAMB, Mista Fabian Benjamin, Ministan ya kuma bada umarnin hukunta duk wata makaranta ko cibiyar jarrabawar kwamfuta (CBT) da aka kama da aikata Laifin musamman a wuraren da ake kira miracle centres.

Mista Benjamin ya ce, “Cibiyoyin da aka samu da hannu a cikin wannan laifi za a cire su daga jerin wuraren da aka amince da su domin gudanar da jarrabawa, sannan za a hana su sake karɓar jarabawa har na wasu shekaru.”

Advertisement

JAMB ta ce sauran hukumomin shirya jarabawa kamar WAEC, NECO da NABTEB za su bi sahu wajen aiwatar da irin wannan hukunci kan cibiyoyin da ke da hannu a aiwatar da laifin.

Hakazalika, JAMB ta bayyana cewa duk ɗalibin da aka kama da satar amsa za a yi amfani da lambar shaidarsa ta ƙasa (NIN) wajen dakile masa damar sake rubuta wata jarabawa a cikin lokacin hukuncin.

Advertisement

Ta ce wannan mataki yana da tushe a dokar hana satar amsa, wato Sashe na 16(2) na Dokar Satar Amsa, wadda ta ba da dama ga hukumomin shirya jarrabawa su raba sunayen masu laifi domin daukar matakin hadin gwiwa.

A cewar JAMB, wannan doka za ta taimaka wajen dakile yaduwar satar amsa a makarantu tare da dawo da martabar tsarin ilimi a Najeriya.

Advertisement

Hukumar ta bukaci iyaye, malamai da dalibai su dauki wannan mataki da muhimmanci, tare da hadin gwiwar tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin ilimi.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending