News
JAMB Za Ta Yiwa Masu Bukata ta Musamman Rajistar UTME Kyauta
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta sanar da cewa za ta yiwa ɗaliba masu bukata ta Musamman rajistar jarabawar UTME ta shekarar 2026/2027 kyauta.
Sanarwar ta fito ne a cikin jaridar mako-mako ta JAMB da aka wallafa a shafin yanar gizon hukumar, inda aka bayyana cewa shirin zai gudana ta hannun JAMB Equal Opportunity Group (JEOG), wadda ke kula da ɗaliban da ke da bukata ta Musamman.
Rikici Kan Naira 200 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mai Sayar Da Doya Da Kwai A Unguwar Medile Da Ke Kano
Magatakardar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ce shirin zai shafi ɗaliban da ke fama da Down syndrome, Dyslexia, Autism da kuma ADHD. Ya kara da cewa za a ba su littattafan sauti a nau’o’in MP3, WMV da WMA, domin su dace da na’urorin sauraro na zamani.
Oloyede ya bayyana cewa shirin na nufin ba da damar ilimi da daidaito ga dukkan ɗalibai, musamman masu bukata ta Musamman
An fara rajistar UTME ne ranar 26 ga Janairu, kuma za ta ƙare ranar 28 ga Fabrairu.
