Connect with us

News

Rikici Kan Naira 200 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mai Sayar Da Doya Da Kwai A Unguwar Medile Da Ke Kano

Published

on

photo

Wasu da ake zargi yan daba sun kashe wani matashi mai sana’ar soya doya da ƙwai, Sulaiman Muhammad, a Unguwar Medile Turba da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Rahotanni ce lamarin ya faru ne a daren Lahadi, bayan wata musayar yawu da ta ɓarke tsakaninshi da mutanen kan kuɗin doyar Naira 200.

An Gurfanar Da Mutum 9 A Kotu Bisa Zargin Kisan Mutum 150 A Yelwata 

A yayin rikicin, ana zargin ɗaya daga cikin yan daban ya caka wa marigayin wuƙa, lamarin da ya janyo masa mummunan rauni.

Shaidu sun ce Sulaiman Muhammad ya zubar da jini mai yawa kafin daga bisani ya rasu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar yan sandan jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.

Advertisement

 

PREMIER RADIO

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending