News
Za A Fara Rajistar UTME Ranar Litinin – JAMB
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta sanar cewa rajistar UTME 2026 za ta fara ne daga Litinin, 26 ga Janairu, zuwa 28 ga Fabrairu, a dukkan cibiyoyin kwamfuta (CBT) da hukumar ta amince da su a fadin Najeriya.
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka ne a Legas yayin taro da Kwamishinonin Ilimi na jihohi. Ya ce sayar da takardar neman rajista (e-PIN) zai fara daga 19 ga Janairu kafin fara rajistar kai tsaye.
Jami’an ‘Yansanda Sun Kama Amarya Bisa Zargin Kashe Mijinta Da Maganin Ɓera A Jigawa
Farfesa Oloyede ya kara da cewa zaɓin jarabawar gwaji (mock) za a rufe a ranar 16 ga Fabrairu, yayin da sayar da takardun neman Direct Entry (DE) zai fara daga 2 ga Maris har zuwa 25 ga Afrilu.
Shugaban hukumar ya yi gargadi cewa duk cibiyoyin CBT da ba a iya sa ido a kan su daga hedkwatar JAMB ba za su samu biyan kuɗi, kuma rajistarsu a soke su.
Haka nan, ɗalibai ba su da bukatar biyan kowanne ƙarin kuɗi ga cibiyoyin CBT; kuɗin rajista da JAMB ta amince da su kaɗai ake biya.
