Connect with us

News

Jami’an ‘Yansanda Sun Kama  Amarya Bisa  Zargin Kashe Mijinta Da Maganin Ɓera A Jigawa 

Published

on

Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin kashe mijinta ta hanyar sanya guba a abincin rana a ƙauyen Gauza, da ke Ƙaramar Hukumar Jahun a jihar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya fitar a ranar Asabar.

Advertisement

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, lokacin da wani sabon ango ya rasu bayan cin abincin da ake zargin matarsa ce ta sa masa guba.

Kaduna: Dakarun Soji Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Maraban Rido

Advertisement

Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa marigayin ya ci abincin rana ne a gidansu, kafin daga bisani ya kamu da matsananciyar rashin lafiya. An gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa yayin da ake masa jinya.

Bayan faruwar lamarin, ‘yansanda sun ce jami’ansu na sashen Jahun sun fara bincike nan take, inda suka kama matar marigayin a matsayin babbar wadda ake zargi da aikata laifin.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin amsa tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa iyayenta ne suka tilasta mata auren marigayin, abin da ta ce ya jefa ta cikin halin damuwa da ya kai ta ga aikata wannan mummunan aiki.

A halin yanzu, Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Jigawa ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse, domin zurfafa bincike.

Advertisement

Rundunar ta ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending