Connect with us

News

Kaduna: Dakarun Soji Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Maraban Rido

Published

on

Picsart 26 01 24 18 02 18 355 scaled

Sojojin Rundunar 1 Division ta Sojojin Nijeriya sun dakile wani hari da ake zargin ‘yan bindiga sun kai a wani yanki na Jihar Kaduna, inda aka hallaka mutum ɗaya daga cikin maharan.

Bayanan da PRNigeria ta fitar sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren 22 ga Janairu, 2026, bayan da jami’an tsaro suka samu rahoton gaggawa kan wasu ‘yan bindiga da suka shiga ƙauyen Anguwan Fulan, a yankin Maraban Rido, inda suka kwashi dabbobin  mazauna garin.

Advertisement

Tsohon Ɗan Majalisar Jihar Kano, Zubairu Madobi, Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Da samun bayanan sirri, sojoji suka tura dakaru zuwa yankin, inda suka yi masu kwanton ɓauna a hanyoyin da ake zargin maharan za su bi wajen tserewa.

Advertisement

A lokacin da aka yi arangama da su, sojojin sun buɗe wuta, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka watse. Daya daga cikinsu ya rasa ransa yayin musayar wutar.

Majiyoyin soji sun ce bayan arangamar ta farko, dakarun sun ci gaba da bincike a dazuzzukan yankin, ciki har da Dajin Kankomi, domin hana ‘yan bindigar sake haɗuwa ko kai wani sabon hari.

Advertisement

Rahotanni sun ce an sake samun wata arangama a kusa da Anguwan Sarki, inda hakan ya ƙara tarwatsa yunkurin tserewar maharan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending