Connect with us

News

Majalisar Wakilai Ta Gano Cushe A Sabbin Dokokin Haraji Da Tinubu Ya Sanya Wa Hannu

Published

on

Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya ya ce ya gano wasu sauye-sauye da bambance-bambance tsakanin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya musu hannu.

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton bincike na musamman da Majalisar Wakilai ta kafa, biyo bayan zargin cewa an yi cushe ko sauya wasu sassa a cikin sabbin dokokin harajin ƙasar.

Advertisement

Tsohon Ɗan Majalisar Jihar Kano, Zubairu Madobi, Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Zargin ya fara ne bayan wani ɗan majalisar, Abdulsamad Dasuki, ya bayyana damuwarsa kan yadda dokokin harajin suka fito bayan amincewar majalisa, lamarin da ya sa aka kafa kwamitin bincike.

Advertisement

Kwamitin ya ce bayan kwatanta takardun da Majalisar Wakilai ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa a hukumance, an gano sauye-sauye masu muhimmanci, musamman a cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya ta 2025.

Daga cikin canje-canjen da aka lura da su akwai rage adadin kuɗin da ake buƙatar bayyanawa, da kuma tilasta masu biyan haraji su ajiye wani kaso na kuɗinsu, tare da bai wa hukumomin tara haraji ƙarin iko na ɗaukar matakai ba tare da umarnin kotu ba.

Advertisement

Rahoton ya kuma nuna cewa an cire ikon Majalisar Tarayya na sanya ido kan aiwatar da dokokin haraji da aka wallafa, abin da kwamitin ya ce na iya haifar da matsala ga tsarin dimokuraɗiyya da rarraba iko.

Majalisar Wakilai ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace bayan kammala nazari kan rahoton kwamitin kamar yanda FRI ta ruwaito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending