Connect with us

News

Kashi 67.35% Na Dalibai Sun Samu Kiredit 5 Ciki Har Da Turanci Da Lissafi — Hukumar NECO

Published

on

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) ta 2024, inda dalibai 57,114 suka samu maki biyar ko fiye, ciki har da Turanci da Lissafi, wanda ya kai kaso 67.35%.

Advertisement

Jimillar daliban da suka yi rajista don jarabawar sun kai 86,067, inda aka gudanar da jarabawa a fannonin karatu 29.

Dan Majalisa Ya Fadi Hukumar Da Ke Daukar Nauyin Boko Haram

NECO ta bayyana cewa jimillar dalibai 84,799 ne suka zauna jarabawar.

Advertisement

Baya ga hakan, dalibai 70,711, wanda ke wakiltar kaso 83.39%, sun samu maki biyar ko fiye ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an kama dalibai 6,160 da laifin satar jarabawa, yayin da aka haramta wa masu sa ido 7 daga jihohin Oyo, Ogun, Legas, Ebonyi, da Cross River saboda taimakawa wajen magudia jarabawa.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending