Connect with us

News

Dan Majalisa Ya Fadi Hukumar Da Ke Daukar Nauyin Boko Haram

Published

on

images (1)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan majalisar Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da daukar nauyin ayyukan kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS.

Advertisement

Mr. Perry ya yi wannan zargi yayin zaman farko na wani kwamitin majalisar mai suna: Karamin kwamiti kan tabbatar da aikin ofishin Government Efficiency (DOGE).

Zargin Rashawa: Jami’in Binance Ya Ambaci Wasu ‘Yan Majalisar Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kafa ofishin DOGE wanda Elon Musk ke jagoranta da nufin rage kashe kudaden gwamnatin Amurka.

Advertisement

Trump ya dade yana sukar USAID, yana zarginta da cin hanci, yayin da Elon Musk ya kira hukumar “mafaka ga masu tsatstsauran ra’ayi.”

Scott Perry ya ce USAID tana kashe dala miliyan 697 duk shekara, wanda ya hada da tura kudade zuwa makarantu da sansanonin horas da mayaka.

Advertisement

Ba a gabatar da kwararan hujjoji don tabbatar da zargin ba, yayin da masu suka ke ganin an yi hakan ne domin kashe hukumar.

 

Advertisement

Ana zargin USAID da daukar nauyin ta’addanci

A cewar dan majalisar, kasafin kudi na shekara-shekara na USAID wanda ya kai dala miliyan 697, tare da aika kudade zuwa makarantu na addini (madrasas), ya tallafa wa sansanonin horas da mayaka da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Advertisement

“Kuɗin harajinku, dala miliyan 697 na kowace shekara, suna taimaka wa ISIS, al-Qaeda, Boko Haram, ISIS Khorasan, da sansanonin horas da ‘yan ta’adda,” inji dan majalisar.

 

Advertisement

 

An ga dan majalisar a cikin a wani bidiyo mai tsawon minti daya da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda yake jaddada cewa “wadannan kungiyoyin ne suke tallafa wa.”

Advertisement

 

Bai gabatar da hujja don tabbatar da zargin ba, yayin da ‘yan Democrat da dama ke cewa ‘yan Republican na yunkurin bata sunan USAID domin rusa hukumar.

Advertisement

 

Mr. Perry ya kuma zargi kashe dala miliyan 136 na hukumar USAID wajen gina makarantu 120 a Pakistan, yana ikirarin cewa ba a gina makarantun ba.

Advertisement

 

Ya kuma zargi USAID da kashe dala miliyan 840 cikin shekaru 20 da suka wuce a shirye-shiryen ilimi a Pakistan.

Advertisement

 

Scott Perry ya ce akwai dala miliyan 60 da aka ware don tallafawa mata a Afghanistan duk da hana mata fitowa fili da gwamnatin Taliban ta yi.

Advertisement

 

Ayyukan ‘yan ta’adda a Najeriya

Advertisement

Gwamnatin Najeriya na fafutukar yakar ta’addanci musamman a Arewa maso Gabas inda Boko Haram da ISWAP ke kai hare-hare.

 

Advertisement

Hare-haren Boko Haram da ISWAP sun dau tsawon kusan shekaru 20 ba tare da an ga karshensu ba, inji rahoton Premium Times.

 

Advertisement

Duk da kungiyar ISWAP na samun tallafi daga kasashen waje, Boko Haram ta dogara ne kan harajin tilas da take kakabawa garuru da kuma fashin da take yi a kauyuka.

 

Advertisement

A shekarar 2020, wata kotu a Hadaddiyar Daular Larabawa ta yanke wa wasu ‘yan Najeriya shida hukuncin daurin shekaru kan taimaka wa Boko Haram da kudi.

 

Advertisement

Hukuncin ya taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen gano wasu mutanen da k

e da alaka da wannan tallafin.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending