Connect with us

News

An Gano Matar Da Aka Ce An Yi Garkuwa Da Ita Tare Da Masoyinta A Otal Bayan Neman Kuɗin Fansa

Published

on

Married 768x559

Wata mata mai aure mai suna Oluchi, wadda aka yi zargin cewa an yi garkuwa da ita a Jihar Edo, ta shiga hannu bayan jami’an ’yan sanda sun gano ta tare da wani mutum da ake zargin masoyinta ne a wani otal da ke Jihar Delta.

Tun da farko, iyalan matar sun sanar da hukumomin tsaro cewa an yi garkuwa da ita ne a yankin Ikpoba Hill da ke Ƙaramar Hukumar Ikpoba-Okha a Jihar Edo.

Advertisement

Ilimi Ne Babban Makamin Daƙile Ta’addanci — Ministan Tsaro

Rahotanni sun ce bayan ɓacewar ta, mutanen da suka yi ikirarin su ne masu garkuwa da ita sun nemi a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa. Daga baya kuma sun rage adadin zuwa Naira miliyan 20.

Advertisement

Lamarin ya sa iyalanta da abokansu suka fara neman taimakon jama’a domin tara kuɗin da ake buƙata don ceto ta.

Sai dai binciken da jami’an ’yan sanda suka gudanar ya sauya alkiblar lamarin, bayan da suka gano matar a wani otal da ke Ubiaroko a Jihar Delta tare da wani mutum.

Advertisement

Wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta ce jami’an tsaro sun gano inda suke ne bayan bibiyar wata lambar waya da ake zargin tana da alaƙa da ɗaya daga cikin waɗanda ake bincike.

“Jami’an ’yan sanda sun bi sawun lambar wayar har zuwa wani otal a Ubiaroko, inda suka tarar da mutumin da kuma matar da aka ce an yi garkuwa da ita,” in ji majiyar.

Advertisement

Diyarta, Anita, ta bayyana mamakinta da takaicinta kan yadda lamarin ya kaya a cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

Ta ce iyalansu sun shiga damuwa matuƙa tun bayan ɓacewar mahaifiyarta, kuma sun yi duk mai yiwuwa wajen neman taimako domin ceto ta.

Advertisement

“An sanar da mu cewa an sako mahaifiyata. Daga baya muka gano cewa tana da hannu a cikin wannan lamarin. Duk abin da muka yi, mun yi ne domin ganin ta dawo lafiya,” in ji Anita.

Ta ƙara da cewa ba a biya ko sisin kwabo a matsayin kuɗin fansa ba, inda ta ce kuɗaɗen da aka tara za a mayar wa waɗanda suka bayar da gudummawa.

Advertisement

Anita ta kuma yi zargin cewa masu bincike sun shaida musu cewa mahaifiyarta da mutumin da aka kama tare sun shirya yadda za su samu wani ɓangare daga kuɗaɗen da aka tara.

A cewarta, abin da ya faru ya jefa iyalansu cikin ruɗani da baƙin ciki, musamman ganin cewa mahaifinta na fama da matsalolin lafiya.

Advertisement

Haka kuma, wata ƙungiyar mata mai suna Harmony Ladies Club ta nuna takaicinta kan lamarin, bayan da ta bayar da tallafi da goyon baya ga iyalan matar lokacin da aka yi zargin sace ta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, CSP Moses Yamu, ya ce an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a cikin al’amarin.

Advertisement

Ya ce bincike na ci gaba domin gano cikakken yadda aka shirya lamarin da kuma rawar da kowane wanda ake zargi ya taka.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending