Connect with us

News

Kwanaki 40 Bayan Kisan Maharba A Edo: Iyalan Mamata Na Neman A Biya Su Diyya

Published

on

1746657977373

Kwanaki 40 bayan kisan maharba 16 daga Jihar Kano a garin Uromi, Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa Maso Gabas a Jihar Edo, iyalan mamatan sun ci gaba da kira ga gwamnati da ta biya su diyya tare da tabbatar da adalci.

An kashe maharban ne a watan Maris yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa Kano domin gudanar da bikin Sallah Ƙarama. Maharban sun fito daga ƙananan hukumomin Kibiya, Rano da Bunkure na Jihar Kano.

Advertisement

Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Dubu 13 Da 500 – Badaru Abubakar

A wani taro da iyalan suka gudanar a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Kibiya, an gudanar da karatun Alƙur’ani domin roƙon rahamar Allah ga mamatan. Iyalin sun bayyana damuwa kan yadda gwamnati ta gaza daukar matakin da ya kamata a game da lamarin.

“An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga cikin bakin ciki da wahala. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana halin da ake ciki,” in ji Malam Bala Dutse, mahaifin ɗaya daga cikin mamatan.

Advertisement

Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin maharban da aka kashe, ta bayyana irin ƙuncin rayuwar da take ciki tare da ’ya’yanta uku.

“Sun ce za su ba mu adalci, amma har yanzu babu komai. Har yaushe za mu jira?” in ji ta.

Advertisement

A baya, gwamnonin Kano da Edo — Abba Kabir Yusuf da Monday Okpebholo — sun ziyarci iyalan mamatan inda suka yi alkawarin tallafi da adalci. Haka kuma, Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Sai dai, iyalan sun ce har yanzu ba su ga wani ci gaban bincike ko tallafi ba.

Advertisement

Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya bayyana cewa an riga an kama wasu da ake zargi da hannu a kisan, kuma an tura su Abuja. Sai dai ya bukaci a gudanar da shari’a a bainar jama’a domin tabbatar da adalci da gaskiya.

Wannan kisa ya sake haskaka matsalar rikice-rikicen ƙabilanci da ke barazana ga zaman lafiya a ƙasar. Masana da dama na ganin rashin cikawa da gwamnati ke yi ga alkawuran ta na kara dagula lamarin.

Advertisement

Iyalan mamatan sun bayyana cewa ba za su yi shiru ba har sai an tabbatar da adalci.

“Za mu ci gaba da magana har sai an yi mana adalci,” in ji Malam Bala Dutse.

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending