News
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Tsare Gudaji Kazaure Kan Zargin Karbar Naira Miliyan 70 Daga Emefiele
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta tsare tsohon dan majalisar wakilai, Honarabul Gudaji Kazaure, bayan da ya amsa gayyata zuwa ofishinta da ke Kano.
Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa bayan isarsa ofishin, jami’an hukumar suka tsare shi, kuma yanzu haka ana shirin tura shi zuwa Abuja domin ci gaba da bincike.
Kwanaki 40 Bayan Kisan Maharba A Edo: Iyalan Mamata Na Neman A Biya Su Diyya
Bayanan da muka samu sun nuna cewa hukumar EFCC na binciken Kazaure ne kan wasu kudade da suka kai Naira miliyan 14 da aka samu sun shiga asusunsa a wani lokaci a shekarar 2019.
Sai dai DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa akwai wani zargi da ke nuna cewa Kazaure ya karbi Naira miliyan 70 daga hannun tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Kawo yanzu dai EFCC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin, amma ana sa ran karin bayani zai bayyana nan gaba.
