Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye A Gidajen Rediyo Da Talabijin

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da yada duk wani shirin siyasa da ake watsa shi kai tsaye a gidajen rediyo da talabijin na jihar.

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ma’aikatar ta saba gudanarwa da shugabannin kafafen watsa labarai.

Advertisement

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Tsare Gudaji Kazaure Kan Zargin Karbar Naira Miliyan 70 Daga Emefiele

A cewar sanarwar da Daraktan Harkokin Musamman na ma’aikatar, Malam Sani Abba Yola ya fitar, an dauki wannan mataki ne don dakile yaduwar kalaman da za su iya tayar da zaune tsaye a cikin al’umma.

Kwamishina Waiya ya ce manufar dakatarwar ita ce kare zaman lafiya da mutuncin al’adun jama’a da kuma daidaiton addinai a Kano, ba wai don hana ‘yan adawa bayyana ra’ayinsu ba.

Advertisement

“Ba mu dauki wannan mataki don murkushe ‘yan adawa ba. Manufarmu ita ce kare martabar al’ummarmu da dabi’un addini na jihar Kano,” in ji shi.

A taron, an kuma yanke sabbin matakai da suka hada da tilasta wa duk wani bako da zai halarci shirin siyasa a kafofin yada labarai, sanya hannu kan alkawarin kauce wa kalaman batanci da zagi ga kowa, ciki har da addini da al’ada.

Advertisement

An umarci masu gabatar da shirye-shirye da su guji tambayoyi ko maganganu da za su iya haddasa batanci ko cin mutuncin wani bangare na al’umma.

Kwamishinan ya ce an fara ganin tasirin wadannan matakai, inda ya bayyana cewa amfani da kalaman batanci a gidajen rediyo da talabijin ya ragu.

Advertisement

“Mun dauki matakan wayar da kai ga masu gabatar da shirye-shiryen siyasa da masu sharhi a kafafen yada labarai da ma Limaman Juma’a, domin sakonnin siyasa su rika zuwa cikin mutunci ba tare da cin zarafi ba,” in ji Waiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending