Connect with us

News

Wani Ɗan Kasuwa Ya Rasu Yayin Rikici Da Ɗansa A Abuja

Published

on

crime control 768x432

Wani al’amari mai tayar da hankali ya faru a Abuja bayan da wani ɗan kasuwa mai suna Mista Adimike Godwin ya rasa ransa sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakaninsa da ɗansa a gidansa da ke unguwar Guzape.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da daddare bayan saɓani ya kaure tsakanin marigayin da ɗansa mai shekaru 19, wanda aka ce yana yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashin shirin NYSC.

Advertisement

AKCCC Ta Shirya Taron Haɗuwar Classmates Karo Na 4

Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne bayan mahaifin ya tambayi ɗansa kan wasu halaye da ya nuna, ciki har da dawowarsa gida cikin dare daga wajen shaƙatawa.

Advertisement

An kuma rawaito cewa rikicin ya ƙara kamari ne sakamakon wasu matsaloli da suka shafi harkokin kuɗin kasuwanci, lamarin da ya janyo cacar baki mai zafi tsakanin su.

Shaidu sun bayyana cewa yayin rikicin ne aka soki marigayin da wuƙa, wanda hakan ya jawo masa munanan raunuka.

Advertisement

Maƙwabta sun ce sun ji hayaniya daga gidan kafin su sanar da jami’an tsaro, amma ana zargin matashin ya tsere kafin isowar ’yan sanda.

Jami’an tsaro sun samu marigayin kwance cikin jini, inda aka garzaya da shi Babban Asibitin Karu domin ceto rayuwarsa, sai dai likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Advertisement

Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa rundunar ta fara gudanar da bincike mai zurfi kan mutuwar.

Ta ce rundunar ta kama mutum biyar, ciki har da wani ɗan uwa, domin taimaka wa bincike da gano musabbabin aukuwar lamarin.

Advertisement

Marigayin, wanda ke harkar kasuwancin gidaje, an ce ya saba zirga-zirga tsakanin Legas da Abuja saboda harkokinsa na kasuwanci.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending