News
AKCCC Ta Shirya Taron Haɗuwar Classmates Karo Na 4
An shirya gudanar da taron haɗuwar tsofaffin ɗaliban makarantar Aminu Kano Community Commercial College (AKCCC) karo na huɗu domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin classmates.
A cikin wata sanarwa da masu shirya taron suka fitar, sun bayyana cewa ana gudanar da irin wannan taro ne duk shekara domin tuna lokutan karatu da kuma ƙara dankon zumunci tsakanin tsofaffin ɗaliban makarantar.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Satar Ragunan Layya 18
Sanarwar ta ce za a gudanar da taron ne ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026 da misalin ƙarfe 2:00 na rana a Hall ɗin makarantar AKCCC kamar yadda aka saba.
Masu shirya taron sun yi kira ga dukkan classmates da su fito domin ba taron muhimmanci tare da tabbatar da halarta, suna masu cewa kasancewar kowa tare na daga cikin abubuwan da ke ƙara armashi da nasarar taron.
Haka kuma, sun roƙi waɗanda suka samu sanarwar da su taimaka wajen isar da saƙon ga sauran classmates domin kowa ya samu damar halartar taron.
Sun bayyana fatan cewa taron zai kasance cikin farin ciki, ƙauna da ci gaba da ɗorewar zumunci a tsakanin mahalarta.
A ƙarshe, masu shirya taron sun yi addu’ar Allah Ya haɗa kowa lafiya tare da sanya taron ya gudana cikin nasara da albarka.
Shuwagabannin Taron:
M sani yalwa
Alkasim sagir
Abba nafi u dan baba
Abdullahi tasiu
Junaidu mahmud ahmad
Abdallah mustafah
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
