News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Matashi Kan Yaɗa Bidiyon Harin Ƴan Bindiga Na Ƙarya A TikTok
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta kama wani mutum bisa zarginsa da yada wani faifan bidiyo na harin ‘yan bindiga na karya a shafukan sada zumunta da nufin samun mabiya ta yanar gizo.
Jaridar mai sharhi kan sha’anin tsaro Zagazola Makama ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Mayun nan, bayan da wani mai suna Ayinla Sodiq daga Obasanjo Ota, ya kai wanda ake zargin mai suna Qowiy Oloyede mazaunin hanyar Oriya Sokoto Atan Ota ofishin ’yan sanda.
Yadda Sana’ar Kiwon Kaji Ke Zama Tushen Arzikin Mata A Arewacin Najeriya
Mai ƙarar ya zargi matashin da kirkira tare da yada wani bidiyo na yaudara a shafin TikTok, inda ya yi ikirarin cewa ’yan bindiga sun mamaye al’ummar Atan Ota da ke Jihar.
Jaridar ta ce baturen ƴan sanda na yankin ya yi wa wanda ake zargin tambayoyi, inda ya amsa laifinsa na kirkirar bidiyon don ƙara samun mabiya a shafukan sada zumunta.
Wanda ake zargin ya ce bidiyoyi biyu kadai ya taba yi ɗaya ya ɗora shi a ranar Litinin, ya yin da ɗayan kuma ya dora a ranar Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin ’yan sanda sun gano hotuna da bidiyoyi daban-daban masu alaƙa da labarin ƙarya a lokacin binciken farko.
Rundunar ta ce za ta aike da wanda ake zargin zuwa sashen binciken Manyan laifuka na Jihar, domin ci gaba da gudanar da bincike.
Rundunar ta yi gargaɗi mazauna jihar game da yaɗa labaran ƙarya da za su iya haifar da fargaba da tashin hankali a tsakanin al’umma, tare da yin kira ga jama’a da su dunga tabbatar da gaskiyar labari kafin su yada shi.
