News
Yadda Sana’ar Kiwon Kaji Ke Zama Tushen Arzikin Mata A Arewacin Najeriya
A da, mata da dama a Arewacin Najeriya kan yi kiwon kaji ne domin biyan bukatun gida kawai, amma a yanzu sana’ar ta koma wata babbar hanyar samun kudin shiga da tallafa wa iyali, musamman a wannan lokaci na tsadar rayuwa.
Matan aure, zawarawa, aure da kuma ‘yan mata na daga cikin wadanda suka rungumi sana’ar kiwon kaji domin samun abin dogaro, duk kuwa da kalubalen tsadar abincin kaji, cututtuka da rashin jari da ke addabar harkar.
Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 12 A Hanyar Kano Zuwa Katsina
Bincike ya nuna cewa kiwon kaji na daga cikin sana’o’in noma da suka fi saukin shiga ga mata a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, saboda ba ya bukatar babban jari kamar sauran sana’o’in noma.
Rahotanni sun bayyana cewa bangaren kiwon kaji na bayar da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin Najeriya, yayin da mata ke kula da mafi yawan kananan gidajen kiwon kaji a yankunan karkara.
Wasu daga cikin matan da ke gudanar da sana’ar sun bayyana cewa duk da wahalhalun da suke fuskanta, sana’ar na taimaka musu wajen ciyar da iyalansu da kuma rage radadin tsadar rayuwa.
Halima Abdullahi, daya daga cikin masu sana’ar, ta ce duk da irin kalubalen da ke tattare da kiwon kaji, tana samun riba mai kyau daga sana’ar.
“Wani lokaci mutum kan so ya hakura saboda wahala da tsadar kayan kiwo, amma idan aka yi hakuri akwai anfani sosai. Na samu damar sayen fili tare da taimaka wa mijina saboda wannan sana’a,” in ji ta.
Ita ma Hajiya Zaliha Mohammad Abdullahi ta ce ta shafe sama da shekara 10 tana sana’ar kiwon kaji, inda ta fara da kaji 250 amma yanzu take da sama da kaji 1,000.
“Ko da yake ana samun mace-macen kaji wani lokaci, amma sana’ar na da anfani sosai. Tsadar abinci da kananan kaji na daga cikin manyan matsalolinmu,” kamar yadda ta bayyana.
Amina Habibu, wadda ta fara sana’ar cikin kasa da shekara guda, ta ce ta fara da kaji uku kacal amma yanzu tana da fiye da kaji 50.
“Ina kula sosai da kajina kuma ban taba yin asara ba tun da na fara,” in ji ta.
Fauziyya Abdullahi, wadda ta shafe shekaru takwas tana harkar, ta ce kula da tsafta da tuntubar likitan dabbobi na taimakawa wajen rage yaduwar cututtuka.
“Idan kaza daya ta kamu da cuta, sauran ma na iya kamuwa cikin sauki, shi ya sa muke yin taka-tsantsan sosai,” in ji ta.
Haka ita ma Maijidda Mohammad ta bayyana cewa yin rigakafi tun kaji na kanana na daga cikin hanyoyin kare su daga cututtuka.
“Bana wasa da tsafta da rigakafi saboda cututtukan kaji na saurin yaduwa,” in ji ta.
Masana sun ce idan aka kara tallafa wa mata masu kiwon kaji da jari, horaswa da hanyoyin samun kasuwa, sana’ar za ta kara bunkasa tare da samar da karin ayyukan yi da inganta wadatar abinci a Arewacin Najeriya.
