News
Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 12 A Hanyar Kano Zuwa Katsina
Aƙalla mutum 12 ne suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Gidan Mutum Daya da ke kan hanyar Kano zuwa Katsina.
Rahotanni sun ce hatsarin ya rutsa da wata tirela da kuma motar haya ta Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA), inda motocin biyu suka yi taho-mu-gama da juna da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Lahadi.
Kotu Ta Yanke Wa Matasa Biyu Hukuncin Kisa Kan Rikicin Ƙwallon Ƙafa A Kano
Majiyoyi sun bayyana cewa mutum shida, ciki har da direban motar, sun mutu nan take a wurin hatsarin, yayin da wasu shida suka rasu bayan an kai su asibiti domin ceto rayukansu.
Baya ga haka, mutum biyu na ci gaba da karɓar magani a Babban Asibitin Katsina sakamakon raunukan da suka samu, yayin da aka sallami wasu mutum biyar bayan likitoci sun tabbatar da lafiyarsu ta daidaita.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan wannan lamari, yana mai cewa hatsarin ya jefa jihar cikin jimami.
Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan tare da bai wa iyalansu juriyar wannan babban rashi. Haka kuma ya yi kira ga direbobi da su riƙa kiyaye dokokin hanya domin rage yawaitar hatsurra a manyan hanyoyin Najeriya.
