Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Matasa Biyu Hukuncin Kisa Kan Rikicin Ƙwallon Ƙafa A Kano

Published

on

kotu 768x390 (1)

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kashe wani matashi sakamakon rikicin da ya samo asali daga cacar baki kan wasan ƙwallon ƙafa.

Mai shari’a Musa Muhammad Dahuru ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin a kotun mai lamba ta 21 da ke Kano.

Advertisement

Gidauniyar Fistula Foundation Ta Nuna Damuwa Kan Hana Masu Yoyon Fitsari Zuwa Asibiti

Waɗanda aka samu da laifin sun haɗa da Yusuf Ahmad Abba, wanda aka fi sani da Ziro Rijiyar Lemo, da kuma Auwal Abdulhamid Bachirawa.

Advertisement

 

Kotun ta ce matasan sun kai wa Ibrahim Umar Mahmud hari bayan wata muhawara da ta kaure a tsakaninsu a ranar 7 ga watan Yunin 2025.

Advertisement

Bayanan da aka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Yusuf Ahmad Abba ya daba wa marigayin wuƙa a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatar da shaidu biyar domin tabbatar da tuhumar da ake yi musu, yayin da lauyan waɗanda ake ƙara ya roƙi kotun ta sassauta hukuncin.

Advertisement

Sai dai kotun ta bayyana cewa ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, inda ta same su da laifin kisan kai tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

Advertisement

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending