News
Gidauniyar Fistula Foundation Ta Nuna Damuwa Kan Hana Masu Yoyon Fitsari Zuwa Asibiti
Gidauniyar Fistula Foundation ta bayyana damuwarta kan yadda wasu iyaye da masu kula da marasa lafiya ke hana mata masu fama da lalurar yoyon fitsari zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, duk da irin wayar da kan jama’a da ake ci gaba da yi.
Shugaban gidauniyar, Baba Musa Isah, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin bikin ranar masu fama da lalurar yoyon fitsari, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin wayar da kai da tallafa wa masu fama da cutar.
Falaloli 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Arafa
Ya ce gidauniyar ta samu nasarar yi wa mata sama da 345 aikin gyaran yoyon fitsari kyauta, inda ya bayyana cewa kashi 90 cikin 100 daga cikinsu sun samu lafiya.
“Akwai waɗanda suka warke gaba ɗaya, yayin da waɗanda har yanzu ba su samu cikakkiyar waraka ba ake ci gaba da kula da su tare da tausaya musu,” in ji shi.
Baba Musa Isah ya bayyana ranar a matsayin rana ta tausayi, jimami da kuma wayar da kai ga al’umma kan cewa ana iya warkewa daga cutar yoyon fitsari idan aka kai marasa lafiya asibiti cikin lokaci.
Ya buƙaci iyalai da su daina barin mata masu fama da lalurar zama a gida ko bin bokaye da ’yan bori, yana mai cewa ana gudanar da aikin gyaran cutar kyauta kuma ana samun waraka.
Ya ƙara da cewa gidauniyar na zagaya jihohin Najeriya domin gudanar da ayyukan tiyatar gyaran yoyon fitsari, tare da gode wa gwamnatocin jihohi bisa haɗin kai da bayar da damar amfani da asibitoci domin gudanar da ayyukan.
A nata ɓangaren, cibiyar kula da masu yoyon fitsari ta Kwalli da ke Jihar Kano ta bayyana cewa cibiyar na ƙarƙashin Ma’aikatar Mata ta jihar, kuma tana kula da marasa lafiya tare da koya musu sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwarsu bayan sun warke.
Da take jawabi ta bakin Daraktar Walwalar Mata ta ma’aikatar, Halima Ibrahim BB-Faruk, kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Kano ta ce gwamnatin jihar na ƙoƙari wajen kula da lafiyar da walwalar masu lalurar, ciki har da samar musu da abinci sau uku a rana.
Ta ce gwamnatin na ci gaba da shirye-shiryen wayar da kai a ƙananan hukumomin jihar domin rage kyamar da ake yi wa masu fama da lalurar.
“Suna buƙatar kulawa da tausayi, domin ba da son ransu suka kamu da wannan lalura ba,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa ma’aikatar na aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tallafa wa masu fama da cutar.
Wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar tallafin kuwa sun bayyana godiyarsu ga gidauniyar da masu ruwa da tsaki bisa irin kulawar da suke ba su ba dare ba rana.
