News
Falaloli 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Arafa
Ranar Arafa na daga cikin ranaku mafiya daraja a Musulunci, kasancewarta daya daga cikin kwanaki goma na farkon watan Zulhijja da Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana a matsayin mafi falala cikin kwanakin shekara.
A ranar ne alhazai ke taruwa a filin Arafa domin gudanar da tsayuwar Arafa, wanda shi ne ginshikin aikin Hajji, yayin da sauran musulmi da ba su samu damar zuwa Hajji ba ake karfafa musu gwiwar azumi da yawaita ibada domin cin gajiyar falalar ranar.
Farfesa Adamu Gwarzo: Jagoran Da Ke Daga Darajar Ilimi Da Ci gaban Dan Adam A Afirka
Malamai sun bayyana cewa ranar na dauke da rahama, gafara da ‘yanta bayi daga wuta, tare da kasancewarta rana mafi dacewa da yin addu’a da neman gafarar Allah.
Ga wasu daga cikin falalolin ranar kamar yadda hadisai suka tabbatar:
- Shi ne wuni mafi falala a cikin shekara.
- A wunin Allah Ya cika addinin Musulunci.
- Allah Ya yi rantsuwa da wunin a cikin Suratul Buruj.
- A cikin wunin Allah na ’yanta bayi daga wuta zuwa aljanna.
- A wunin alhazai ke taru a wuri daya domin tsayuwa a filin Arafa
- A ranar Allah kan yi alfahari da bayinsa da suka halarci tsayuwar Arafa.
- Babu aikin Hajji ga mahajjacin da bai yi tsayuwar Arafa a cikin wunin ba.
- Azumtar wunin na kankare zununban shekara da ta gabata da mai wanzuwa.
- Wuni ne mai albarka da zama silar mutum ya samu aljannah.
- A irin wannan yini Manzon Allah (SAW) ya yi hudubarsa ta bankwana
- A cikin wunin ake samun mafi alherin addu’a. Manzon Allah ce shi da dukkanin manzannin da suka gabata sun yi addu’ar da ta fi kowacce falala: “La ilaha illal Lahu wahdaHu la sharika laHu laHul mulku wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli shai’in kadir.”
- Yana da kyau a kara da dukkan ayyukan alheri, gaida mara lafiya, karatun Al Kur’ani
