News
’Yansanda Sun Cafke Mutum 7 Kan Garkuwa Da Yaro Mai Shekara 8 A Katsina
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu wajen garkuwa da wani yaro mai shekara takwas a cikin birnin Katsina.
Bayanan da rundunar ta fitar sun nuna cewa jami’an sabon sashen yaƙi da manyan laifuka (VCRU) ne suka gudanar da samame na musamman wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargin bayan samun sahihan bayanan sirri.
Alƙalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu Bayan Faɗuwa A Gidansa Da Ke Kano
A cewar ’yan sanda, an sace yaron ne a ranar 13 ga watan Mayu yayin da yake dawowa gida daga makarantar Islamiyya, lamarin da ya jefa iyalansa cikin fargaba.
Rahoton ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyayen yaron tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 50 kafin daga bisani aka sasanta kan Naira miliyan 17 domin sakin yaron.
Binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya kai ga kama mutum shida ciki har da wanda ake zargin shugaban ƙungiyar ne, Nura Aliyu, wanda aka bayyana a matsayin maƙwabcin iyayen yaron. Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da Abubakar Aminu, Ibrahim Muhammad, Iliyasu Sani, Abubakar Muhammad da Abdullahi Isma’il.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu yayin bincike tare da bayyana sunan wani abokin aikinsu mai suna Abdul, wanda har yanzu yake tsere.
Haka kuma, jami’an tsaro sun ƙwato Naira miliyan 7.5 da ake zargin ragowar kuɗin fansar ne, tare da wata mota ƙirar Peugeot 307 da kuma babur ƙirar Boxer.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai jaddada ƙudirin rundunar wajen ci gaba da murƙushe masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata manyan laifuka a jihar.
