News
Alƙalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu Bayan Faɗuwa A Gidansa Da Ke Kano
Wani Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, Justice Mohammed Nasir Yunusa, ya rasu bayan ya faɗi a falonsa a ranar Alhamis da yamma.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yanke jiki ne a gidansa, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, sai dai daga bisani likitocin suka tabbatar da rasuwarsa.
Zan Dauki Matakin Shari’a A Kan Duk Wanda Ya Kara Cewa Ina Bai Wa ‘Yan bindiga Kariya —Sheikh Gumi
Majiyoyi daga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce an gudanar da jana’izarsa a ranar Juma’a bisa koyarwar addinin Musulunci.
Daraktar Yaɗa Labarai ta Babbar Kotun Tarayya, Catherine Oby Christopher, ta tabbatar da rasuwar alkalin, tana mai cewa ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano bayan an kai shi domin ceto rayuwarsa.
Zan Dauki Matakin Shari’a A Kan Duk Wanda Ya Kara Cewa Ina Bai Wa ‘Yan bindiga Kariya —Sheikh Gumi
Marigayi Justice Mohammed Nasir Yunusa ya kasance ɗaya daga cikin alkalan da suka jagoranci manyan shari’o’i masu ɗaukar hankali a Najeriya, ciki har da shari’o’in da suka biyo bayan zaɓen shekarar 2023 da suka shafi takarar ‘yan jam’iyyar Labour Party a wasu sassan ƙasar nan, har da ta tsohon gwamnan jihar Abia, Alex Otti.
Abokan aikinsa da na kusa da shi sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙwazo, dattijo mai tawali’u da kuma wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci da gaskiya a harkokin shari’a.
