Connect with us

News

‎Taimakon Soji Daga Kasashen Waje Ba Shi Ne Mafita Ta Dindindin Ga  Gakalubalen Tsaron Najeriya Ba ‎ ‎—SHEHU SANI

Published

on

IMG 20240717 WA0016 640x430

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce taimakon soji daga kasashen waje ba shi ne mafita ta dindindin ga gakalubalen tsaron Najeriya ba.

‎Shehu Sani, ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan rahotannin hare-haren sojin Amurka, a kan ƴan ta’addan ISIS a jihar Sakkwato, inda rundunar Sojin Amurka a Afrika (AFRICOM), ta ce an aiwatar da shi ne a matsayin aikin haɗin gwuiwa tare da hukumomin Nijeriya.

Advertisement

Majalisar Wakilai ta umurci a sake wallafa sabbin dokokin haraji

‎Sai dai Sanata Sani, ya gargaɗi gwamnati da kada ta dogara da ƙasashen waje domin magance matsalolin tsaron ƙasar nan, yana mai jaddada cewa samun zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa dole ne ya samo asali daga ƴan ƙasa.

‎“Ƙasashen waje na iya taimakawa, amma ba za su iya yaƙar mana dukkan matsalolinmu na har abada ba,” in ji Shehu Sani.

Advertisement

‎Tsohon sanatan ya kuma musanta ra’ayin da ke cewa hare-haren ƴan ta’adda na shafar mabiya addini guda ɗaya ne kawai, yana cewa wannan fahimta ba daidai ba ce.

‎A baya-bayan nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya bayar da umarni ga sojojin ƙasarsa da su kai hare-hare kan ƴan ta’addan ISIS a Arewa maso Yammacin Nijeriya, yana mai cewa an aiwatar da su ne domin dakile ayyukan ta’addanci.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending