Connect with us

News

Kotun Ghana Ta Daure ‘Yar Najeriya Watanni 15 Kan Cin Zarafin ‘Yarta ‘Yar Shekara 9

Published

on

IMG 20251226 101058 623x381 1

Wata kotu a ƙasar Ghana ta yanke wa wata ‘yar Najeriya, Beauty Alakwe, hukuncin daurin watanni 15 tare da aikin wahala a Gidan yari, saboda cin zarafin ‘yarta ‘yar shekara tara a yankin Ashanti.

Kotun Circuit Court da ke Tafo a birnin Kumasi ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, bayan ta same Alakwe, mai shekaru 34, da laifin jikkata yarinyar a Duase kusa da Kenyasi, kamar yadda rundunar ‘yan sandan yankin Ashanti ta bayyana.

Advertisement

‎Taimakon Soji Daga Kasashen Waje Ba Shi Ne Mafita Ta Dindindin Ga  Gakalubalen Tsaron Najeriya Ba ‎ ‎—SHEHU SANI

Baya ga hukuncin daurin, kotun ta kuma ci tarar Alakwe Cedi 6,000 na Ghana. Sai dai kasancewar ta gaza biyan tarar, an tura ta gidan yari na Central Prison da ke Kumasi .

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Nuwamba, bayan wani mazaunin yankin, tare da goyon bayan wakilin majalisar yankin, suka kai rahoton cin zarafin ga hukumomi.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY REPORT

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending