News
KAROBA Ta Nemi Taimakon Sarkin Karaye Kan Sake Buɗe Unity College Bayan Shafe Sama Da Shekaru Uku A Rufe
Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Karaye (KAROBA) ta Ƙasa ta nemi goyon bayan Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz Karaye, wajen ganin an sake buɗe Unity College Karaye, dake Jihar Kano wadda aka rufe tun kusan shekara huɗu da suka gabata.
Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, ACI Murtala Uba Sule Burum Burum (Rtd.), ne ya jagoranci mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa zuwa fadar Sarkin a wata ziyara da suka kai ranar Asabar, 25 ga Yuli, 2026.
A cewar shugaban ƙungiyar, ziyarar ta kasance domin gaisuwar ban girma da kuma taya Sarkin Karaye murnar cika shekara biyu da hawa karagar mulki. Ya ce sun kuma yi amfani da damar wajen tattauna batun sake buɗe Unity College Karaye, wadda rufe ta ya haifar da koma baya ga harkar ilimi a yankin.
Burum Burum ya bayyana cewa KAROBA na ci gaba da gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ganin Gwamnatin Jihar Kano ta sake buɗe makarantar. Haka kuma ya sanar da naɗa Mai Martaba Sarkin Karaye a matsayin Babban Uban Ƙungiyar (Grand Patron).
Da yake jawabi, Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz Karaye, ya nuna damuwa kan yadda makarantar ta shafe shekaru a rufe, yana mai cewa hakan ya haddasa lalacewar gine-gine da sauran kayayyakin makarantar.
Sarkin ya tabbatar wa shugabannin KAROBA da cikakken goyon bayansa, tare da alƙawarin yin aiki da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an gyara makarantar tare da sake buɗe ta cikin gaggawa.
Ya kuma bayyana cewa Masarautar Karaye za ta naɗa wakilai da za su yi aiki tare da ƙungiyar wajen bibiyar wannan ƙuduri har sai an cimma nasara.
Har ila yau, Sarkin ya amince da karɓar matsayin Babban Uban Ƙungiyar, yana mai jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafa wa KAROBA a duk wani yunƙurin da zai amfani ilimi da ci gaban al’ummar Karaye.
Bayan kammala ziyarar fadar Sarkin, shugabannin KAROBA sun kai ziyara harabar Unity College Karaye, inda suka duba halin da makarantar ke ciki. Sun bayyana takaicinsu kan irin lalacewar da suka gani, sakamakon tsawon lokacin da makarantar ta shafe ba tare da gudanar da harkokin karatu ba.
Ƙungiyar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗa kai da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sake buɗe Unity College Karaye da dawo da martabarta a matsayin ɗaya daga cikin manyan makarantun sakandire a Jihar Kano.
