Connect with us

News

Yawaitar Garkuwa Da Manoma Na Iya Haifar Da Karancin Abinci A Najeriya —Rahoto

Published

on

Spread the love

Karuwar satar mutane da ake yi wa manoma a Jihohin Kwara, Filato, Taraba, Neja, da sauran jihohin tsakiyar Nijeriya na kara haifar da fargabar matsalar karancin abinci a shekarar 2026.

Rahoton Jaridar LEADERSHIP  ya gano cewa, a cikin jihohin da abin ya shafa, an tilasta wa manoma dakatar da ayyukan lokacin rani bayan an sace su da dama a bakin koguna da wuraren shuka. Haka zalika, an bar girbin amfanin gona a gonaki yayin da muhimman wuraren samar da abinci suka zama babu komai.

‎Ba Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Aiwatar Da Dokokin Haraji A Janairun 2026 ‎ ‎— Gwamnatin Tarayya  ‎

Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da aka yi gargadin cewa fiye da mutum miliyan 34.7 a Nijeriya na iya fuskantar karancin abinci sosai zuwa tsakiyar shekarar 2026, bisa ga sabon binciken Cadre Harmonisé.

An gano rashin tsaro mai dorewa a matsayin daya daga cikin manyan dalilan da ke kara tsananta matsalar abinci.

Advertisement

Manoma sun ce hare-haren na rage ingancin tsarin samar da amfanin gona wanda yake da matukar muhimmanci ga samar da shinkafa, masara, da kayan lambu a kasa. Binciken farko da kungiyoyin manoma suka yi ya nuna cewa akwai manyan tangarda a matakin samar da amfanin gona a kauyuka yanayi da zai iya kara matsin tattalin arziki yayin da kasar ke matsowa zuwa shekarar 2026.

Shugaban Kungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), Muhammad Magaji, ya shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa rikicin tsaro ya riga ya sauya yanke shawarar dubban manoma da ke shirin yin ayyukan lokacin rani. Ya lura cewa wasu kungiyoyi gaba daya suna barin gonaki da ke tallafawa amfani na gida da samar da kayayyaki.

A cewar shugaban kungiyar manoma, barazanar ta yi tsanani har ma masu matsakaitan aiki na samar da amfanin gona suna rage yawan filayensu mataki da ya bayyana cewa zai rage ikon kasa na tabbatar da isasshen abinci a shekarar mai zuwa.

A watan Nuwamba, Gwamnatin Tarayya ta yi murnar raguwar farashin abinci, inda Ministan Noma da Tsaron Abinci, Abubakar Kyari, ya danganta wannan ci gaba da tsundumar gwamnatoci a kasuwa ta hanyoyi masu manufa. A cewar Ministan, raguwar farashin abinci a cikin kayayyaki da dama na nuna cewa tsunduma gwamnatoci a samarwa, isar da kayan aiki, da daidaita kasuwa yana aiki.

Advertisement

“Ko da yake ba mu kai inda muke so ba tukuna, wannan yanayi mai kyau yana tabbatar da cewa muna kan hanyar da ta dace,” in ji Kyari ga mahalarta Taron Majalisar Kasa na 47 Kan Noma da Tsaron Abinci a Jihar Kaduna.

Sai dai, Magaji ya lura: “Rashin tsaro ya riga ya fara shafar mambobinmu, musamman wadanda ke noma a lokacin rani, saboda mutane da dama ana kama su yayin aikin gona a lokacin rani yayin aikin masara, shinkafa, ko wasu amfanin gona. Abin takaici, saboda rashin tsaro, hakan yana matukar shafar mambobinmu yanzu.”

Ya kara da cewa: “Idan yanayin tsaro ya inganta, da yawa daga cikin manoma za su koma ayyukan noma. Idan kana shirin noma ne kawai a kan hekta biyar zuwa goma, ingantaccen tsaro zai iya karfafa ka ka fadada zuwa hekta 20, 30, ko ma 60. Abin da ake bukata kawai shi ne Gwamnatin Tarayya ta inganta yanayin tsaro.”

Masu ruwa da tsaki a harkar noma suna da irin wadannan damuwa. Sun yi gargadi cewa alamun farko na karancin abinci a kasa baki daya sun fara bayyana a hauhawar farashin kayan aiki da rashin tabbas mai yawa tsakanin manoma.

Advertisement

Yawancin kananan manoma wadanda ke bayar da fiye da kashi 70 cikin 100 na amfanin gida yanzu ba sa iya ci gaba da samarwa yadda ya kamata, abin da masana ke jin tsoron zai iya raunana tsarin abinci na kasa.

Shugaban Kungiyar Harkokin Noma ta Nijeriya (NABG), Arc Kabir Ibrahim, ya yi gargadin cewa rashin isassun kayan aiki, tsadar sufuri, da raguwar samar da su a karkara, yana kawo tasiri ga farashin kasuwa.

Ibrahim ya shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa tsadar gudanar da ayyukan noma na tilasta wa kananan manoma shiga cikin talauci mai zurfi, wanda ke hana su samun damar farfadowa da sauri don hana karancin abinci a kasa baki daya zuwa shekarar 2026.

“Karuwar rashin tsaro na iya zama babbar barazana ga cimma burin samun isasshen abinci. Farashin abinci da ba za a iya saya ba saboda karancin kaya da tsadar samarwa na nuni da babban karanci, kuma wannan yanayi na iya kara tsananta hauhawar farashi,” in ji Ibrahim.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa: “Tsadar kayan aiki mai yawa na haifar da hauhawar farashin abinci a kowane lokaci, kuma rashin tsaro karin barazana ce ga cimma ikon sarrafa abinci da samun isasshen abinci.

Kara shiga talauci tsakanin kananan manoma tabbas zai shafi samar da abinci, kuma shekarar 2026 na iya zama shekara mai matukar wahala ga ‘yan Nijeriya.”

Sauran masu ruwa da tsaki sun nace cewa hanya daya tilo da za a iya kauce wa matsalar karancin abinci mai tsanani ita ce dawo da tsaro a yankunan da ake samar da abinci a Nijeriya. Sun bayyana cewa da zarar an tabbatar da tsaro, manoma za su kara samar da abinci, masu zuba jari za su koma, kuma samar da abincin zai farfado. Ba tare da daukar mataki nan take ba, sun yi gargadin cewa shekarar 2026 na iya zama daya daga cikin shekarun da suka fi wahala wajen samar da abinci a tarihin Nijeriya na baya-bayan nan.

Kungiyar Ma’aikata, karkashin jagorancin Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta yi gargaDin cewa Nijeriya na iya fuskantar tashin farashin abinci idan manoma da aka tilasta wa barin gonakinsu ba za su iya komawa al’ummominsu ba.

Advertisement

A yayin da yake jawabi kan halin kasa a taron Majalisar Zartarwa ta kasa a Abuja, Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamared Festus Osifo, ya yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa rashin tsaro ya wuce lamuran da suka kebe kuma yanzu yana barazana ga daidaito na kasa da farfadowar tattalin arziki.

Osifo ya danganta rugujewar ayyukan noma da rikicin rashin tsaro, yana mai jaddada cewa babu wasu manufofin tattalin arziki da za su yi nasara idan manoma ba za su iya shuka ko girbi ba. Ya kara da cewa gwamnati dole ne ta magance rikicin daga tushe ta hanyar taimaka wa manoma su koma gonakinsu.

“A kasuwa, farashin kaya ba sa sauka. Idan ka je kasuwa da Naira 100,000, ba za ka dawo da komai ba. Gwamnati ta tarayya, jihohi, da kananan hukumomi su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa farashin kayayyaki yana karkashin kulawa. Dole su tabbatar cewa manoma za su iya komawa gona, saboda sai manoma sun koma gona ne kawai za su iya samar da sabbin amfanin gona don kawo kasuwa,” in ji shi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *