Connect with us

News

An Hallaka Wani Matashi Saboda Cajar Waya A Anambra

Published

on

images (2)
Spread the love

Wani matashi mai suna Chisom ya rasa ransa sakamakon wata takaddama da ta barke tsakaninsa da ɗan uwansa kan Cajar wayar hannu a garin Ihiala da ke Jihar Anambra, a kudancin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Disamba, bayan wata muhawara da ta rikide zuwa fada tsakanin Chisom da ɗan uwansa, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba.

An Hallaka Wani Matashi Saboda Cajar Waya

Wani rubutu da aka wallafa a dandalin sada zumunta na Confra Naija, wanda ke wayar da kan jama’a kan yaki da kungiyoyin asiri, ya bayyana cewa Chisom ya taba ba wa ɗan uwan nasa Cajar waya a baya, amma rikici ya barke ne a lokacin da Chisom ya koma domin karɓar Cajar.

A cewar rahoton, muhawarar ta rikide zuwa fada mai tsanani, inda ake zargin ɗan uwan Chisom da caka masa wuka a wurare da dama, lamarin da ya janyo masa munanan raunuka.

Advertisement

Rahoton ya ƙara da cewa mahaifin wanda ake zargi, wanda shi ne baffan Chisom, ya shiga cikin rikicin, abin da ya kara ta’azzara lamarin har ya kai ga mutuwar matashin.

Bayan faruwar lamarin, rahotanni sun ce ‘yan sanda sun kama ɗan uwan mamacin, yayin da wasu matasa a yankin suka kona gidan baffan nasa, lamarin da ya janyo tashin hankali a cikin al’umma.

A wani bidiyo da aka gani, an hango gawar mamacin kwance a gadon asibiti, yayin da ‘yan uwansa ke kuka.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Rundunar ‘Yansandan Jihar Anambra ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, duk da kokarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a, Tochukwu Ikenga.

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *