News
Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Sabon Shirin Wayar Da Kan Matasa Kan Rajistar Zaɓe
Kwamitin Wayar Da Kan Dalibai Da Matasa Kan Rajistar Zaɓe (CVR) a Jihar Kano ya ƙaddamar da wasu sabbin dabaru domin ƙara wayar da kan matasa da ɗalibai kan muhimmancin yin rajistar zaɓe da shiga harkokin dimokuraɗiyya.
An cimma matsayar ne a wani taron kwamitin da aka gudanar ranar Laraba a ɗakin karatu na Jihar Kano da ke Ahmadu Bello Way, ƙarƙashin jagorancin Mai Bai Wa Gwamna Shawara Kan Harkokin Dalibai, Dakta Yusuf Jibrin Oyoyo.
Jihar Kano Ce Ke Kan Gaba Wajen Yawan Masu Sabbin Rajistar Katin Zabe 441,845
Da yake jawabi a taron, Dakta Oyoyo ya ce lokaci ya yi da matasa za su ƙara taka rawa a harkokin siyasa da zaɓe, yana mai jaddada muhimmancin yin rajistar zaɓe, karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC) da kuma amfani da shi a lokacin zaɓe.
Ya bayyana cewa kwamitin ya amince da yin aiki tare da manyan ƙungiyoyin ɗalibai domin yaɗa saƙonnin wayar da kai a makarantu da cibiyoyin ilimi daban-daban na jihar.
Ƙungiyoyin da aka tsara yin aiki tare da su sun haɗa da NANS, JCC, shugabannin SUG, NAKSS, NAPS, NAUS da NANCES, tare da wasu ƙungiyoyin ɗalibai da ke aiki a jihar.
A cewar kwamitin, haɗa hannu da waɗannan ƙungiyoyi zai taimaka wajen isa ga dubban matasa da ɗalibai domin ƙarfafa su su shiga rajistar zaɓe da sauran harkokin dimokuraɗiyya.
Haka kuma, kwamitin ya amince da faɗaɗa shirinsa zuwa matakin ƙananan hukumomi ta hanyar haɗin gwiwa da Majalisar Matasa ta Jihar Kano, shugabanninta a ƙananan hukumomi 44 da kuma shugabannin matasa na jam’iyyar APC a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
Kwamitin ya kuma amince da shigar da ƙungiyoyin taimakon kai (Self-Help Groups) cikin wannan shiri domin ƙara wayar da kai a matakin al’umma, unguwanni da mazaɓu.
Mambobin kwamitin sun bayyana kwarin gwiwar cewa wannan tsari zai taimaka wajen ƙara yawan matasan da za su yi rajistar zaɓe tare da shiga harkokin siyasa da dimokuraɗiyya a faɗin jihar.
A ƙarshe, Dakta Oyoyo ya yaba wa membobin kwamitin bisa jajircewarsu, tare da kira gare su da su gaggauta aiwatar da shawarwarin da aka cimma domin samun nasarar shirin.
