Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis A Matsayin Ranar Hutu 

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Alhamis, 12 ga Yuni, a matsayin ranar hutu domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2025.

Sanarwar ta fito ne daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ta bakin Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Magdalene Ajani, a ranar Lahadi.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Diyya Kan Soke Hawan Sallah

Ministan ya taya ’yan Najeriya murnar cika shekaru 26 da komawar ƙasar mulkin farar hula, yana mai yabawa da juriya da ƙwazo da al’umma ke nunawa wajen ganin dimokuraɗiyya ta dore.

Ya ce, “a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Najeriya na ci gaba da mutunta ƙa’idodin dimokuraɗiyya, kuma ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa wajen tsara harkokin siyasa, tattalin arziki da rayuwar yau da kullum.”

Advertisement

Gwamnatin ta kuma bukaci ’yan ƙasa da su ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending