Connect with us

News

Kano Da Sauran Jihohi Za Su Fuskanci Mamakon Ruwa Na Tsawon Kwana Uku – NIMET

Published

on

images (5)

Hukumar kula da yanayi ta ƙasa, NIMET, ta yi hasashen cewa za a iya samun mamakon ruwan sama mai haɗe da tsawa da iska a wasu jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano, daga ranar Lahadi zuwa Talata, 11 ga Yuni, 2025.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa ana sa ran wannan ruwan zai fara ne da gajimare a yawancin yankuna, kafin daga bisani a samu sauyin yanayi zuwa ruwan sama mai ƙarfi.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis A Matsayin Ranar Hutu 

Jihohin da za su fi fuskantar wannan ruwan sun haɗa da Kano, Katsina, Taraba, Adamawa, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe da Bauchi.

Sauran su ne Abuja, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Benue da Plateau.

Advertisement

NIMET ta shawarci al’umma su share magudanan ruwa domin kaucewa ambaliya, musamman a yankunan da ruwa ke taruwa cikin sauƙi.

Haka kuma, hukumar ta ja hankalin manoma da masu ababen hawa da su lura da yanayi, su kuma bi hanyoyin kariya domin kaucewa haɗurran da sauyin yanayi zai iya haifarwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending