News
Sanata Barau Ya Kai Ziyara Kasuwar Waya Ta Farm Centre, Ya Ba Da Tallafi Naira Miliyan 200
DAGA ABBA ANWAR, KANO
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Ibrahim Jibrin, ya kai ziyara Kasuwar Waya ta Farm Centre dake Kano, domin jajanta wa ’yan kasuwar da gobara ta shafa a ranar Juma’ar da ta gabata.
A yayin ziyarar da ya kai ranar Lahadi, Sanata Barau ya ba da tallafin kayan kasuwanci da ya kai kimanin Naira Miliyan 200, domin rage asarar da gobarar ta yi wa ’yan kasuwar.
Kano Da Sauran Jihohi Za Su Fuskanci Mamakon Ruwa Na Tsawon Kwana Uku – NIMET
Sanatan ya bayyana wannan gobara a matsayin gwaji daga Allah, inda ya ce wannan kasuwa na da matuƙar muhimmanci wajen samar da aikin yi ga matasan jihar Kano.
“Da na samu labarin gobarar nan, na ji matuƙar damuwa. Nan take na kuduri aniyar zuwa domin jajanta wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. Ofishina zai ba da tallafi na kayan kasuwanci da ya kai Naira Miliyan 200,” in ji Sanata Barau.
Baya ga tallafin kayan kasuwanci, Sanata Barau ya ce zai ba da motar kirar Hilux guda daya, babura guda biyar, da fitilun titi na hasken rana guda dubu daya (1,000), domin inganta tsaron kasuwar.
Haka kuma, ya bayyana shirin gina gada ta tsallaka titi domin sauƙaƙa zirga-zirga da tabbatar da tsaron masu amfani da titin.
Yan Kasuwar Waya ta Farm Centre, sun nuna godiya ga Sanata Barau bisa wannan ziyara da tallafin da ya bayar.
Sun kara da cewa Sanata Barau ba wai Sanatan Kano ta Arewa ba ne kadai, har ma shi jagora ne ga al’umma baki ɗaya. Muna godiya sosai ga wannan taimako,
