Connect with us

News

Akwai yiwuwar samun ruwan sama na tsahon kwanaki 3 A Najeriya —NiMet

Published

on

images (5)

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a wasu sassan ƙasar daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli zuwa Lahadi.

Cikin wani saƙon gargaɗi da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce za a fuskanci yanayi na saukar ruwan sama a wasu jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Borno da Yobe da Kaduna da Bauchi da kuma jihar Gombe.

Advertisement

Haka kuma hukumar ta ce za a samu matsakaicin ruwan sama da tsawa a wasu sassan jihohin Adamawa da Yobe da Sokoto da Zamfara da Bauchi da Borno da Gombe da Jigawa da Kaduna da kuma jihar Taraba.

 ICPC Zata Gurfanar Da Shugaban KANSIEC A Gaban Kotu

Hukuma ta NiMet ta kuma yi hasashen samun ruwan saman a wasu sassan jihohin Plateau da Nasarawa da Abuja da kuma Benue.

Advertisement

 

 

Advertisement

PRNIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending