News
NiMet Ta Yi Hasashen Jihohin Da Za Su Fi Samun Ruwan Sama Mai Yawa

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta ce akwai jihohi shida da ake sa ran za su fi fuskantar ruwan sama a bana fiye da sauran sassan ƙasar nan.
Jihohin su ne Bayelsa, Legas, Akwa Ibom, Rivers, Cross River da Delta, inda ake sa ran za su samu ruwan sama na tsawon kwanaki 250 zuwa 290.
Boko Haram Ta Sake Kai Hari Kan Sansanoni Biyu Na Soji A Borno
NiMet ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da ta fitar ranar Litinin kan hasashen ruwan sama na shekarar 2025.
Rahoton ya ce wasu jihohi da za su biyo baya wajen samun yawan ruwan sun haɗa da Ogun, Oyo, Ekiti, Osun, Ebonyi, Anambra, da Enugu, waɗanda ake sa ran za su samu kwanaki 200 zuwa 250 na ruwan sama.
Haka kuma, jihohin Nasarawa, Neja, Kogi, Benue, Filato, Kwara, da Abuja na daga cikin waɗanda za su samu ruwan sama tsakanin kwanaki 150 zuwa 200.
A bangaren Arewacin ƙasar kuwa, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Zamfara, Borno, da Yobe za su samu kwanaki 110 zuwa 150 na ruwan sama.
NiMet ta bukaci jama’a da su sanya a gaba wannan hasashe domin shiryawa da kuma kauce wa hadurra da yawan ruwan sama ka iya jawo wa.