News
An Kama Mutum Mai Shekaru 47 Bisa Zargin Cin Zarafin ‘Yar Matarsa Mai Shekaru Biyu A Gombe

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta cafke wani mutum mai suna Mohammed Magaji, dan shekara 47, bisa zargin yin lalata da ’yar matarsa mai shekaru biyu a unguwar Tudun Wada da ke Shamaki Quarters a cikin birnin Gombe.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, yana mai cewa lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Mayu, 2025.
NiMet Ta Yi Hasashen Jihohin Da Za Su Fi Samun Ruwan Sama Mai Yawa
A cewar sanarwar, matar Magaji mai suna Hauwau Usman ce ta kai kara ofishin ’yan sanda da misalin karfe 9:32 na safe, inda ta bayyana cewa mijinta ya dauki yarinyar ya shiga da ita dakinsa kuma ya aikata abin kunya da ita.
“Da samun rahoton, rundunar ta tura jami’anta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka kama wanda ake zargin,” inji DSP Abdullahi.
Ya ce daga nan aka garzaya da yarinyar da wanda ake zargi zuwa Asibitin Kwararru na Gombe domin samun kulawa da tabbatar da sahihancin zargin.
An Kuma Kama Wani Bisa Zargin Lalata da ’Yar Shekara Shida
DSP Abdullahi ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wani mutum mai suna Isah Adamu, dan shekara 35 daga Golkos Quarters, Karamar Hukumar Billiri, bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekara shida.
An ce Adamu ya janyo yarinyar zuwa wani gida da ke Awai Quarters, inda ya aikata lalatar da ita. Uwar yarinyar ce ta kai kara, inda daga bisani jami’an ’yan sanda suka cafke wanda ake zargin.
Shi ma an garzaya da su zuwa Asibitin Kaltungo domin duba lafiyar yarinyar da kuma ci gaba da bincike.
DSP Abdullahi ya kara da cewa a cikin makonnin da suka gabata, rundunar ta kama wasu karin mutane 18 da ake zargin da hannu a laifuka daban-daban a sassan jihar.