News
Manoman Najeriya Sun Yi Asarar Naira Tiriliyan 5 Saboda Manufofin Gwamnati — Rahoto
Rahotanni sun nuna cewa manoman Najeriya sun yi asarar kusan Naira tiriliyan 5 a cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon manufofin gwamnati da suka haddasa raguwar farashin amfanin gona, rashin ingantaccen hasashen yanayi, da kuma matsalolin tsarin kasuwannin Kayan noma.
Kungiyar Foundation for Peace Professionals (PeacePro) ta bayyana hakan a wata sanarwa, inda ta ce bangaren noma a kasar na fuskantar babbar matsala t da ke barazana ga makomar samar da abinci.
Yadda Annobar Tsutsa Ta Ja Mana Asarar Miliyoyi — Manoman Rake A Kano
Babban Daraktan kungiyar, Abdulrazaq Hamzat, ya bayyana asarar a matsayin rushewar jarin noma kai tsaye a hannun manoma, yana mai cewa alkaluman ba su hada da illolin da hakan zai iya haifarwa ga tattalin arzikin kasa gaba daya ba.
“Abin da ya riga ya faru shi ne rushewar jarin manoma. Sauran tasirin za su biyo baya ne daga baya,” in ji shi.
A cewar rahoton, a tsakanin shekarun 2024 da 2025, manoma sun rasa ikon cin gajiyar farashin kayayyakin abinci sakamakon manufofin gwamnati da ba su dace da lokaci ba, matakan takaita farashi, rashin daidaiton kasuwa, da kuma rashin sahihin hasashen yanayi daga Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet).
Rahoton ya ce wadannan dalilai sun tilasta wa manoma sayar da amfanin gonarsu ƙasa da kudin da su kashi, lamarin da ya lalata jarin da ake bukata don ci gaba da noman gaba.
Kungiyar ta ce duk da cewa sama da mutane miliyan 38 ke aiki a bangaren noma a Najeriya, mafi yawan asarar ta fi shafar masu manoman kasuwanci masu samar da abinci zuwa kasuwannin birane.
