Connect with us

News

Karancin Maganin Dafin Maciji Na Kara Jefa Rayukan Jama’a Cikin Hadari A Najeriya

Published

on

Snake venom

Asibitoci da dama a sassan Najeriya na fuskantar karancin maganin dafin maciji , lamarin da ke ci gaba da haddasa mutuwar mutane da nakasa, musamman a yankunan karkara da ke fama da raunin tsarin kiwon lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane miliyan biyar ne ke fuskantar sarar maciji a duk shekara a duniya, inda akalla mutane 100,000 ke rasa rayukansu.

Manoman Najeriya Sun Yi Asarar Naira Tiriliyan 5 Saboda Manufofin Gwamnati — Rahoto

Najeriya na daga cikin kasashen da matsalar ta fi shafa, sakamakon yawaitar macizai masu dafi da kuma rashin wadatattun kayayyakin jinya a asibitoci.

A baya-bayan nan, wata matashiya a Abuja ta rasu bayan da maciji ya sare ta, sakamakon rashin samun maganin dafin maciji a asibitin da aka kai ta. Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda karancin kayan aikin lafiya ke haddasa mutuwar da za a iya kauce wa su.

Wani rahoto da shirin Strike Out Snakebite (SOS) ya fitar ya bayyana cewa kashi 98 cikin 100 na ma’aikatan lafiya a Najeriya na fuskantar kalubale wajen kula da marasa lafiya da maciji ya sare.

Advertisement

Rahoton ya danganta matsalar da karancin magani, jinkirin kai marasa lafiya asibiti, da kuma rashin kayan aiki da horo ga ma’aikatan lafiya.

Haka kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa sarar maciji na haddasa mutuwar mutane kusan 138,000, tare da janyo nakasa ga kimanin 400,000 a duk shekara a fadin duniya.

 

THE GUARDIAN 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending